Ministan ya shaidawa taron manema labarai a birnin Pretoria cewa, tuni kasar ta rubutawa babban sakataren MDD Ban Ki-moon wasika game da hakan, matakin da zai baiwa kasar damar ficewa daga kotun shekara guda bayan babban sakataren MDDr ya samu wannan wasika.
Minista Mashutha ya ce,kasar Afirka ta kudu dai tana fuskantar matsin lamba ne karkashin yarjejeniyar Rome wadda ta kafa kotun ICC, yarjejeniyar da ke tilastawa kasar da ke zama mambar kotun na kama mutanen da ke da dokar kariya, amma kotun ta ke neman kama su.(Ibrahim)