Idriss Déby ya jaddada hada karfin Kasashen Afirka domin tabbatar da tsaron harkokin yankin teku
A jiya Asabar 15 ga wata, shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) a wannan karo, kana shugaban kasar Chadi, Idriss Déby ya bayyana a gun taron koli na musamman kan tsaron harkokin yankin teku na kungiyar AU cewa, kundin da aka cimma a Lome zai ba da gudummawa wajen hada karfin kasashen Afirka da kafa tsarin daidaitawa da sa ido, domin tinkarar barazanar da yankin tekun Afirka ke fuskanta tare da juna.
Shugaba Deby ya kara da cewa, zartas da kundin Lome na nufin cewa, an shiga wani sabon mataki na kiyaye muhallin yankin teku da cimma burin samun dauwamemmen ci gaba a nahiyar Afirka. Yana ganin cewa, albarkatun halittu da karfin raya tattalin arziki da yankin tekun nahiyar Afirka yake da su, sun zama babban tushe na raya tattalin arzikin teku. Wannan kundi zai sa kaimi ga raya cinikayya da yankin teku da samar da moriya da kuma samar da guraben ayyukan yi.(Fatima)