Shugaban sashen kula da harkokin Afirka na cibiyar kula da kayayyakin tarihi na duniya ta hukumar UNESCO Edmond Moukala ya bayyana bayan da ya halarci taron karawa juna sani na kasa da kasa game da kalubalen da ake fuskanta a fannin dokokin yayin tafiyar da harkokin tattalin arziki da cinikayya a nan birnin Beijing, cewa, kafofin yada labarai da dama na wasu kasashe sun soki hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, amma da dama daga cikin mu muna ganin babu adalci a game da sukan, haka kuma babu dalilin yin hakan. Kasancewar ni dan Afirka da ke aiki a MDD, ina ganin hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin biyu wani muhimmin dalili ne na ci gaba da ake samu yanzu da kuma a nan gaba, haka kuma shi ne abin da ke tallafawa dauwamammen ci gaba a duniya."
Har wa yau, mataimakin babban darektan kula da harkokin Afirka na hukumar UNESCO Firmin Edouard Matoko wanda shi ma ya halarci taron, ya amince da muhimmancin hadin gwiwar Sin da Afirka ga ci gaban tattalin arzikin Afirka, kuma ya yi fatan za a mai da hankali wajen bunkasa karfin kasashen Afirka a hadin gwiwar da za a gudanar a nan gaba, musamman ma ta fannin horar da matasan Afirka a kan ilmin sana'o'i.(Lubabatu)