Dangane da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Jumma'a cewa, gamayyar kasa da kasa ne ya dace su yi bayani mai adalci kan kalubalolin da tsaron intanet a duniya ke fuskanta, kasar Sin tana tsaya wa tsayin daka kan yin allah wadai da masu satar bayanai ta kwamfuta, kuma wannan matsala ce da ta gallabi duniya baki daya, don haka ya kamata a hada kai wajen fuskantar ta, domin kiyaye tsaro, zaman lafiya da rashin wata rufa-rufa, haka kuma, idan akwai wata kasa dake kula da tsaron intanet, ya kamata ta shiga hadin gwiwar kasa da kasa kan wannan aikin. (Maryam)