Dangane da wannan batu, Pravin Gordhan ya ce, zai tona asirin wasu kudade da aka boye a wasu asusun bankuna, kudaden da suka kai dallar Amurka miliyan dari biyar, wadanda iyalan wani shahararren dan kasuwa mai suna Gupta ya boye, haka kuma wannan iyali yana da dangantaka ta kusa da shugabannin kolin gwamnatin kasar Afirka ta Kudun.
Dangane da wannan lamari, mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya nuna goyon bayansa ga aniyar Mr. Gordhan a hukunce a jiya Lahadi. (Maryam)