A gun taron manema labarai da aka shirya a wannan rana, Stephane Dujarric ya ce, bayan da ya samu wasikar, sashen kula da harkokin shari'a na MDD ya fara aiki a kan batun. Kasar Afirka ta kudu na daya daga cikin kasashen da suka fara rattaba hannu a kan yarjejeniyar Rome ta kafa Kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa. (Lubabatu Lei)