in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya zanta da Ban Ki Moon game da yaki da ta'addanci
2016-09-23 09:47:52 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya zanta da babban magatakardar MDD Ban Ki Moon, game da batutuwan da suka jibanci yaki da kungiyar nan ta Boko Haram, mai sansani a arewa maso gabashin Najeriya.

Da yake karin haske game da hakan ga manema labarai, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce jagororin biyu sun tattauna ne a ranar Laraba, a gabar da ake ci gaba da babban taron mahawara na MDD karo na 71. Kana batutuwan da suka tabo sun kunshi hanyoyin da mahukuntan Najeriyar ke bi game, da ma ayyukan hadin gwiwar dakarun kasashe makwaftan ta, wajen yaki da kungiyar ta Boko Haram.

Ya ce Ban Ki Moon ya jinjinawa gwamnatin shugaba Buhari, bisa namijin kokarin da ta yi wajen kare hakkin bil'adama, da dokokin 'yan gudun hijira na kasa da kasa a dukkanin matakan soji da take dauka. Kaza lika ya yi na'am da kwazon gwamnatin Najeriyar a fannin yaki da cin hanci, da tabbatar da tsawo, tare da yunkurin ta na farfado da tattalin arzikin kasar.

Bugu da kari babban magatakardar MDD ya yabawa shugaba Buhari, bisa gudummawar sa a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaro, tare da tallafawa ayyukan shiga tsakani, a tashe tashen hankulan dake addabar yankunan yammacin Afirka. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China