Rundunar sojojin ruwan Najeriya za ta karfafa ayyukanta na ba da kariya ga muhimman yankuna na kan hanyoyin jiragen ruwa na kasar, tare da sayen wani jirgin ruwan yaki na kasar Sin domin yaki da ayyukan 'yan tawaye, in ji wani jami'in gwamnati a ranar Laraba.
Kakakin rundunar sojojin ruwan, Cor Ezekobe, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa jirgin ruwan yaki na sintiri sumfurin NNS UNITY na rundunar sojojin ruwan Najeriya, da aka kera a kasar Sin, an kammala kuma ya kama hanyar domin cike rundunar sojojin ruwan Najeriya.
Sabon jirgin ruwan yakin zai karfafa kokorin yaki da manyan laifuffukan teku da shiga cikin ruwan Najeriya ba bisa doka ba, musammun ma da shiga ruwan tekun Guinea, in ji jami'in.
A cewarsa, yankunan da sauran jiragen ruwan yaki ba su kai gare su yanzu ana iya yin sintiri kansu tare da NNS UNITY, lamarin da zai karfafa babu shakka karfi da mayar da martani na rundunar ga dukkan wasu matsalolin tsaro na cikin ruwan Najeriya.
NNS UNITY ya bar kasar Sin a ranar Laraba kuma ana jiran zuwansa a Najeriya a farkon makon watan Nuwamba. (Maman Ada)