in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gidaje 300 karamar girgizar kasa ta shafa a jihar Kaduna
2016-09-16 12:12:41 cri
Hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya NEMA, ta ce a kalla gidaje 300 ne karamar girgizar kasar da ta auku a jihar Kaduna ta shafa, inda wasu daga gidajen suka rushe yayin da wasu kuma suka tsattsage.

Musa Ilallah shi ne jagoran hukumar mai kula da yankin arewa maso yammacin kasar, ya kuma bayyana cewa karamar girgizar kasar wadda ta auku a yankin Jaba a farkon wannan mako, ta sanya ma'aikatan hukumar ta fara gudanar da ayyukan ceto, ko da yake dai a cewarsa, ba a samu rahoton asarar rayuka sakamakon aukuwar lamarin ba.

Jami'in ya kara da cewa ma'aikatan hukumar ta NEMA na ci gaba da zagayawa sassan yankin, domin tattara bayanai game da hakikanin barnar da girgizar kasar ta haifar. Ya kuma bukaci al'ummun yankin da su kwantar da hankalin su, kasancewar daukacin hukumomin da batun ya shafa na yin duk mai yiwuwa don ganin an tallafa musu.

Hukumar ta NEMA dai na jiran karin bayanai daga masana a fannin binciken yanayin kasa, domin sanin matakai na gaba da ya dace a dauka. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China