A wata sanarwar da ministan watsa labarai da al'adu na kasar Lai Mohammed ya rabawa manema labarai, ministan ya soki kalaman jam'iyyar adawa ta PDP wadda ke kira ga shugaba Buhari da mukarrabansa da su sake dawo da tattalin arzikin kasar kamar yadda kowa ya san shi a baya kafin su hau karagar mulki a watan Mayun shekarar 2015.
Sanarwar ta ce, kalaman jam'iyyar adawar tamkar kora-kunya ne da hauka, da nufin dauke hankalin gwamnati daga kokarin da take yi na ceto kasar daga halin da ta shiga.
Ministan ya ce, gwamnati za ta ci gaba da karbar shawarwari masu ma'ana, domin ceto kasar daga halin da jam'iyyar ta PDP ta cusa kasar a ciki.
Lai Mohammed ya kara da cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana aiki ba dare ba rana domin farfado da tattalin arzikin kasar. Kuma za ta ci gaba da yaki da matsalar cin hanci da rashawa. (Ibrahim Yaya)