in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwanton baunan kungiyar Boko Haram ya kashe sojojin Nijar guda biyar
2016-09-22 10:11:24 cri
Sojojin Nijar guda biyar sun mutu kana wasu goma sha biyar suka jikkata a yayin da wata tawagar sintiri ta hadin gwiwa tsakanin sojojin Nijar da sojojin Chadi ta ci karo da kwanton baunan kungiyar Boko Haram a yankin Malafatori dake Najeriya, kusa da iyaka da Nijar, a cewar wata majiyar tsaro a ranar Laraba.

A cewar gidan rediyo Amfani mai zaman kansa dake birnin Nijar da ya bayar da labarin a tsakiyar ranar Laraba, kana wata majiyar tsaro dake wurin ta tabbatar da labarin, ta nuna cewa an isar da wadanda suka jikkatan asibitin jihar Diffa inda suke samun jinya sosai.

Bayan wasu hare haren da kungiyar Boko Haram ta kai a makon da ya gabata a Toumour da kuma Gueskerou, dake jihar Diffa dake Kudu maso gabashin kasar, kusa da Najeriya, rundunar sojojin Nijar da kuma dakarun hadin gwiwa na Nijar da Chadi sun gudanar da ayyukan kakkabewa da suka taimaka wajen kawar da 'yan ta'adda guda talatin da takwas da suka boye a wannan yankin na Diffa.

Wadannan ayyukan soja na cigaba da gudana a yanzu haka a yankin, in ji wata sanarwar hedkwatar sojojin Nijar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China