Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a jiya Alhamis, kakakin ta Rabe Abubakar, ya bayyana bidiyon da wani yunkuri da kungiyar ta Boko Haram ke yi na nuna har yanzu tana da sauran tasiri.
Sanarwar ta kara da cewa, ga alama bidiyon shi ne dai wanda kungiyar ta fitar a shekarar 2014, wanda kuma a wannan lokaci aka yi wa kwaskwarima. Rabe Abukakar ya kara da cewa sabon bidiyon ya sake nuna irin hali na rauni da Boko Haram ke ciki, don haka ba zai taba haifar da wata fargaba ko zama barazana ga dakarun kasar ba.
Yankin arewa maso gabashin Najeriya dai ya sha fama da tashe tashen hankula masu alaka da ayyukan mayakan Boko Haram cikin kusan shekaru 6 da suka gabata. (Saminu Hassan)