in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta bayyana babban ci gaban da ta samu wajen yaki da Boko Haram
2016-09-21 12:50:13 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar a ranar Talata cewa, kasarsa ta samu babban ci gaba a yakin da take yi da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, da take kai munanan hare-hare a arewa maso gabashin wannan kasa dake yammacin Afrika.

A albarkacin muhawara ta shekara-shekara ta babban taron MDD, mista Buhari ya shelanta cewa, Najeriya ta cimma nasarori masu muhimmancin gaske a niyyar da ta dauka ta murkushe kungiyar Boko Haram, wanda karfinta na kai hare-hare a matsayin wata kungiyar ta'addanci ya ragu sosai.

A wadannan watanni na baya-bayan nan, hare-harensu na boma-bomai sun tsaya jehi jehi kan wurare masu sauki, in ji shugaban Najeriya tare da tabbatar da cewa, ta wani bangare kasarsa na gudanar da wannan yaki bisa girmama hakkin dan Adam da dokokin kasa da kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China