Mr. Douglas ya ce an zabi Najeriya cikin kasashe 25, duba da irin kyakkyawar manufar kasar a fannin bunkasa harkokin sufurin sama. Kaza lika matakin zai ba da damar horas da ma'aikata sabbin dabarun wanzar da tsaro da kariya ga rayukan masu amfani da jirage. Har ila yau hakan zai samar da dama ta kwarewa a fannin dakile ayyukan 'yan ta'adda, wadanda sau da yawa kan yi kokarin amfani da kafar sufurin sama, wajen kaddamar da hare hare.
Game da hakan, ministan ma'aikatar sufurin saman kasar Hadi Sirika, ya ce Najeriya za ta samar da kananan kayayyakin bada horo da ake bukata a makarantun. Ya ce bayan kammalar aikin, makarantun za su zamo jigon cimma nasarar kudurin gwamnatin kasar, na kasancewar Najeriya daya daga manyan cibiyoyin zirga zirgar jiragen sama na shiyyar yammacin Afirka. (Saminu Hassan)