in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
U17 ta mata ta Najeriya za ta halarci gasar cin kofin duniya da za a yi a Jordan
2016-09-18 12:56:38 cri
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bayyana a shafinta na yanar gizo cewa, tawagar kasar 'yan kasa da shekaru 17 bangaren mata, za ta halarci gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a yi a kasar Jordan.

Sanarwar hukumar ta bayyana cewa, yanzu haka 'yan wasan na Flamingoes suna samun horo a Abuja, babban birnin kasar. Kuma sun shirya tsaf don halartar wannan gasa da aka shirya gudanarwa daga ranar 30 ga watan Satumba zuwa 21 ga watan Oktoba.

A wani bangare na shirye-shiryen shiga wannan gasa, 'yan wasan na Flamingoes sun yi wasannin sada zumunci a gida.

Tawagar ta Najeriya tana rukuni na 3 ne wato C, inda za su kara da kasashe Brazil, Koriya ta Arewa da kuma Ingila. A ranar 26 ga watan Satumba ne ake sa ran 'yan wasan za su tashi zuwa kasar Jordan. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China