A shekarar 2013, gwamnatin kasar Habasha ta sanar da gina madatsar ruwa ta Renaissance dake kan kogin Blue Nile dake yankin iyaka a tsakanin Habasha da Sudan, domin kara samar da wutar lantarki a kasar da dai sauransu, amma, kasar Masar ta ki yarda da shirin din da gwamnatin Habasha ta fid da, sabo da tana damuwar cewa, idan madatsar ruwan na Renaissance ta kafu, yawan ruwa a karshen kogin Nile zai ragu sosai, lamarin da zai haddasa babbar illa ga tattalin arzikin kasar Masar.
Sabo da haka, kasashen Sudan, Masar da Habasha sun yi shawarwari kan wannan batu sau da dama, amma ba tare da cimma matsaya daya ba. Sa'an nan, cikin shekarar 2015 da ta wuce, wadannan kasashe uku sun kulla wata sanarwar ka'idoji, inda suka amince da gina madatsar ruwa ta Renaissance, a sa'i daya kuma, gwamnatocin kasashen uku sun bukaci a yi nazari kan tasirin da wannan aiki zai haifar wa kasashen da abin ya shafa, domin tabbatar da samun isassun ruwa a kasashensu. (Maryam)