Kotun ta bayyana cewa, Mohamed Morsy ya taba tona asirin kasar Masar wanda ya shafi harkokin soja da sauran batutuwa ga kasar Qatar ta hanyar sakatarensa da kuma mambobin kungiyar 'yan uwan Musulmi a yayin da yake kan kujerar shugaban kasar, lamarin da ya sa, ake yi masa irin wannan zargi na aikata laifin leken asiri da kuma cin amanar kasar, kuma bisa wannan zargin, an yanke masa hukunci iri biyu na daurin rai da rai da na daurin shekaru 15.
Kaza lika, bisa dokokin kasar Masar, tsawon lokacin hukuncin daurin rai da rai ya kai shekaru 25, shi ya sa, gaba daya aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai na shekaru 40.
A watan Yulin shekarar 2013, rundunar sojan kasar Masar ta kori Mohamed Morsy daga mukaminsa na shugaban kasar, wanda shi ne shugaban farko na kasar Masar da jama'ar kasar suka zaba, sa'an nan, an kama shi sabo da wasu tuhume-tuhume da aka yi shi. (Maryam)