Mai taimakawa shugaban kasar Sudan Ibrahim Mahmoud Hamid wanda ya bayyana hakan a yayin taron majalisar kula da harkokin jam'iyya mai mulki ta kasar, ya ce duk da kokarin gwamnati na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, har yanzu bangaren adawa da ke samun goyon bayan kasashen ketare, ba su nuna cewa, da gaske suke ba a kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Jami'in ya ce, bangaren adawar kasar, yana fakewa da wasu dalilai marasa tushe, inda suke yunkurin kawo cikas ga shirin sasantawa, duk da yarjejeniyar da gwamnati ta cimma a lokacin tattaunawar samar da zaman lafiya na kasar.
Ya ce, hanya daya tilo ta hau karagar mulki ita yin zabe, ba wai amfani da makami ba. A watan Janairun 2014 ne shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya kaddamar da shirin sasantawa na kasa, inda aka fara taron a watan Oktoban shekarar 2015 zuwa watan Fabrarirun 2016, kafin daga bisani majalisar dokokin kasar ta amince da shawarwarin da za a gabatar a lokacin taron, da nufin tabbatar da zaman lafiya a kasar. (Ibrahim Yaya)