in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu za ta shiga kawancen kudin kwastan na EAC cikin shekaru uku masu zuwa
2016-09-17 13:49:04 cri
Jiya Jumma'a 16 ga wata, shugaban hukumar kudin kwastan da ciniki ta gamayyar kasashen gabashin Afrika wato EAC, Peter Kiguta ya bayyana cewa, kasar Sudan ta Kudu za ta shiga kawancen kudin kwastan na EAC cikin shekaru uku masu zuwa.

Mr. Kiguta ya bayyana haka ne a yayin taron hana ciniki ba bisa doka ba na yankunan EAC da aka shirya a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Haka kuma, ya ce, an ware shekaru uku ne bisa ga yadda kasashen Ruwanda da Burundi suka yi a lokacin da suka neman shiga kwancen kudin kwastan na EAC, haka kuma, gamayyar ta riga ta yi kasafin kudi domin taimaka wa kasar Sudan ta Kudu wajen shiga kawancen kudin kwastan na EAC. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China