Mista Amer ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai da ya samu halartar ma'aikatan ma'aikatar kula da tattalin arzikin kasar da kuma tawagar IMF a Cairo, inda ya ce, wannan rance bisa tsawon shekaru uku zai kasance wani sashe na shirin tattalin arzikin kasar Masar na makundan kudade na dalar Amurka biliyan 21.
Tun nan da shekaru biyar, babban bankin Masar na fama da dukushewar kudin ajiya na kasashen waje, wanda suka ragu daga farkon shekara ta 2011 zuwa karshen watan Mayun shekarar 2016.
Muhimman hanyoyin shigo da jarin waje a cikin kasar, kamar yawon bude ido, mashigin Suez da kuma kudaden 'yan kasar da ke kasashen waje suke aikowa, sun ragu a shekarun baya bayan nan, a sakamakon haka gwamnatin kasar ta nemi tallafi daga wajen IMF.
Mista Amer ya bayyana cewa, an fara tattaunawar neman tallafin tun yau da shekaru hudu da suka gabata, kuma aka tsaida tattaunawar a tsawon shekaru biyu. Ya kara da cewa, baiwa kasar Masar wannan rance kudaden da IMF za ta yi, ya kasance wata shaidar yarda ga tattalin arzikin Masar, yanzu kuma kasar tana jiran tallafi daga sauran hukumomin kudi na duniya. ( Laouali Souleymane).