in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta fara gwajin na'urar adana bayanan jirgin kasar da ya yi hadari
2016-06-20 10:20:54 cri
Kwamitin bincike game da hadarin jirgin EgyptAir mai lamba MS804, ya fara gudanar da gwajin na'urar adana bayanan jirgin, wacce aka gano bayan afkuwar hadarin.

Sanarwar ta ce, tawagar masu bincike na kasar Masar da kuma kwararru daga kasar Faransa ne suka fara aikin gwajin na'urar, kuma tuni suka fara gwajin na'urar dake adana sauti ta jirgin wato (CVR) da kuma wadda take tattara bayanai (FDR), kana an fara gwajin ne a cibiyar bincike ta kwararrun sojojin kasar.

Sanarwar ta kara da cewar za'a tantance dukkanin bayanan da aka samu masu inganci bayan an kamala aikin.

A ranar Laraba ne, kwamitin binciken ya bayyana cewar an gano sassan jirgin a wasu yankuna bayan ya tarwatse a yankin gabar tekun Mediterranean.

Sai dai bayan kwana guda, kwamitin ya bayyana cewar an gano na'urar adana sauti CVR duk da cewar ta lalace.

Kwamitin ya sanar da cewar duk da kasancewar na'urar tattara sautin ta lalace, amma ana saran sashen dake adana bayanai na na'urar bai samu wata illa ba, wadda kuma shine wuri mafi muhimmaci a jikin na'urar.

Za'a cigaba da gudanar da bincike don gano masabbabin hadarin jirgin, duk da kasancewar akwai dalilan da ake hasashen su ne suka haddasa hadarin, ciki har da zargin 'yan ta'adda ne suka tada bom a jirgin yayin da wasu kuma ke zargin tangardar na'ura ne.

Jirgin saman na EgyptAir Flight MS804, yayi hadari ne bayan ya taso daga birnin Paris zuwa Cairo a ranar 19 ga watan Mayun bara, kuma mutane 66 ne cikin jirgin, daga cikinsu akwai 'yan kasar Masar 30 da kuma mutane 15 'yan kasar Faransa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China