Mai rikon mukamin jami'in MDD a Kenya Siddarth Chatterjee, ya fadawa kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua a Nairobi cewa, tuni kasar Amurka ta kashe kudi kimanin dala miliyan 7 domin aikin wanzar da zaman lafiya a Kenya.
Chatterjee ya ce, MDD ta ware makudan kudade domin amfani da su wajen rage yawaitar rikicin kabilanci daga bangaren kasar Habasha.
Chatterjee ya fada a lokacin taro game da cigaban kasashen shiyyar gabashin Afrika da magance rikice-rikice da tsattsauran ra'ayi cewar, MDD a shirye take ta zuba kudade domin inganta fannonin cigaban rayuwar al'umma musamman samar da ilmi da kiwon lafiya.
Shirin kiyaye zaman lafiyar na hadin gwiwa ne tsakanin MDD da hukumar cigaban kasashen gabashin Afrika IGAD, da kuma kasashen Kenya da Habasha.
Chatterjee ya ce, ana sa ran samun cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali nan da shekaru 5 masu zuwa, kasancewar shugabannin kasashen da abin ya shafa suna daukar matakan da suka dace don warware rikicin ta hanyar siyasa.(Ahmad Fagam)