Jiya Jumma'a 16 ga wata, hukumar kiwon lafiya ta kasar Sudan ta fidda wata sanarwa, inda ta ce, yanzu, an riga an hana yaduwar wata cutar zawayi dake haddasa rasuwar mutane a yankin kudu maso gabashin kasar yadda ya kamata, shi ya sa, babu bukata da hukumar kiwon lafiyar duniya watau WHO ta sa hannu kan lamarin a kasar. Sa'an nan, cikin sanarwar din da Sudan ta bayar, ta yi musu kan labarin yaduwar kwalara da kuma rasuwar wadannan mutane.
Kafin haka kuma, wasu kafofin watsa labarai sun ba da labarin cewa, cutar zawayi ta riga ta haddasa rasuwar mutane kimanin dari daya a jihar Blue Nile, kuma galibi daga cikinsu yara ne, mazaunan wurin suna kuma bayyana damuwar cewa, cutar kwalara ce ta haddasa amai da gudana ga mutanen. (Maryam)