Mambobin kwamitin sulhu sun jaddada cewa ta'addanci, da dukkan nau'o'insa da kuma yadda ake kai shi, na kasancewa daya daga cikin manyan barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, in ji kwamitin a cikin wata sanarwa.
Haka kuma, mambobin kwamitin sulhun sun jaddada bukatar gurfanar da dukkan masu hannu kan ayyukan ta'addanci gaban kotu, bisa tushen kudin MDD da sauran dokokin dake cikin tsarin dokar kasa da kasa, in ji wannan sanarwa.
A nata bangare, gwamnatin Afrika ta Kudu ta bi sahun gamayyar kasa da kasa domin yin allawadai da harin rashin imani da ya faru a kasar Faransa.
Da sunan gwamnati da jama'ar Afrika ta Kudu, shugaba Jacob Zuma ya aike da ta'azziyarsa ga takwaransa na Faransa Francois Hollande, ga gwamnati da kuma al'ummar Faransa, musammun ma iyalan mamatan da kuma wadanda suka jikkata, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar Afrika ta Kudu.
Afrika ta Kudu na tsayawa tsayin daka tare da gamayyar kasa da kasa domin yin Allawadai da duk wasu nau'o'in ta'addanci tare da bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Faransa dake zaman juyayin 'yan kasarta da suka mutu, in ji mista Zuma.
Haka shi, shugaban Amurka Barack Obama, ya yi allawadai a ranar Alhamis da harin Nice na kasar Faransa, tare da bayyana cewa Amurka ta ba da taimakonta ga hukumomin Faransa kan binciken da suke yi kan wannan lamari. (Maman Ada)