Fadan ya kaure ne a ranar 7 ga watan Yuli, tsakanin bangororin sojin da ba sa ga maciji da juna a yaririyar kasar, rahotanni sun ce sama da mutune 270 ne suka hallaka a lokacin tashin hankalin, ciki har da fararen hula 33, kuma sama da mutane 36,000 rikicin ya tilastawa ficewa daga gidajensu.
Wakilin hukumar UNICEF a Sudan ta kudu Mahimbo Mdoe, ya fada cewar, rikicin ya jefa mutane da yawa cikin halin kuncin rayuwa, kuma suna cikin matsananciyar bukatar tallafin abinci, da ruwan sha, da magunguna.
Mdoe, ya ce suna iyakar bakin kokarinsu wajen kai agajin, sai dai abu mafi muhimmanci shi ne yadda za su samu damar shigar da agajin ga mutanen dake cikin matsananciyar bukata, kasancewar akwai wuraren da ba su samun damar shiga.
Babban jami'in ofishin MDD ya fada cewar, a halin yanzu rikicin ya lafa a Juba, bayan shafe kwanaki 5 ana gwamza fada tsakanin bangarorin sojin kasar, sai dai akwai matsalar da jami'an kai agajin ke fuskanta na rashin samun damar shiga wuraren da aka killace mutanen da rikicin ya raba da muhallansu. (Ahmad Fagam)