Cimma kudurin bisa fahimtar juna na bayyana jajircewar gamayyar kasa da kasa na yin aiki tare ba tare da wani wa'adi ba kan yaki da ta'addanci da kaifin kishin addini, in ji mista Ban a cikin wata sanarwar MDD a ranar Jumma'a. Ta'addanci da kaifin kishin addini suna kasancewa babbar bazarana ga zaman lafiya da tsaro, har ma ga dorewar cigaba, ga 'yancin dan adam, aikin jin kai, wannan kuma a dukkan fadin duniya, shiyya da kasa, in ji mista Ban.
Hadin gwiwar yaki da ta'addanci da kuma rigakafin kaifin kishin addini, bisa la'akari da kundin MDD da 'yancin dan adam, na da muhimmaci sosai domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban makomar yara manyan gobe, a cewar babban jami'in MDD.
Ya nuna farin ciki ganin cewa babban taron MDD yayi maraba da kuma gamsuwa da shawarar da ya gabatar game da shirin aikin rigakafi da kaifin kishin addini tare da kuma shawarta wa kasashe mambobin dasu shirya aiwatar da muhimman matakai na shirin, tare da taimakon MDD.
Haka kuma ya bada kwarin gwiwa ga kasashe mambobi dasu cimma shirye shiryen aiki na cikin gida da shiyyoyi domin rigakafin kaifin kishin addini da kuma aiwatar da manyan ginshikai hudu na dabarar yaki da ta'addanci ta duniya daga dukkan fannoni da daidaici. (Maman Ada)