Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya kara da cewar hukumar na shirye-shiryen kai agaji a kan iyakokin Kamaru zuwa garin Banki dake Najeriyar, inda mutane 15,000 da rikici ya raba da muhallansu ke cikin halin matsananciyar bukata.
Ya ce hukumomin ba da agajin sun hada da asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF), da shirin samar da abinci na duniya (WFP), kuma tuni sun fara aiki da mahukuntan Najeriyar domin ba da taimako ga mutane 431,000, ciki har da samar da abinci mai gina jiki ga kananan yara.
Ya kara da cewa, hukumomin ba da agajin na bukatar kudi kimanin dala miliyan 221 domin samar da agaji kafin karshen watan Satumba a yankunan tafki Chadi da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya. (Ahmad Fagam)