Sassan biyu dai za su gudanar da aikin binciken ne a karkashin tekun dake kusa da kasar Masar, domin gano inda tarkacen jirgin suke. Haka kuma, wani jirgin ruwan binciken hanyoyin teku na rundunar sojan tekun kasar Faransa zai shiga wannan aiki.
Hukumar ta Faransa wadda ke aikin bincike da lura da jirgin kirar A320, watau samfurin jirgin saman kasar ta Masar da ya fadi, ta ce kasar Masar ce za ta jagoranci aikin binciken, yayin da ita kuma za ta samar da taimakon fasahohin da za a bukata.
An daina jin duriyar jirgin saman fasinjan ne mallakar kamfanin jiragen saman kasar ta Masar, a yankin bahar Rum a kan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira daga birnin Paris na kasar Faransa. Jirgin na dauke ne da fasinjoji 56, da jami'an tsaro 3, da kuma ma'aikatansa 7.
A kuma ran 20 ga watan nan, rundunar sojan kasar Masar ta sanar da cewa, tawagar aikin ceto ta gano wasu sassan tarkacen jirgin, da gawawwakin fasinjojin, da kayayyakinsu a yankin tekun dake da nisan kilomita 290 a arewacin tashar jiragen ruwa dake Alexander na kasar Masar. (Maryam)