in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin saman Masar ya bace mintuna 20 kafin saukar sa
2016-05-19 20:47:51 cri
Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Marc Ayrault, ya ce jirgin saman fasinjan nan na kasar Masar mai lamba MS804 wanda ya yi layar zama, ya bace ne mintuna 20 kafin saukar sa.

Ayrault ya bayyana hakan ne a filin jirgin sama na birnin Paris, inda ake sa ran zai gana da iyalan fasinjoji 'yan kasar ta Faransa dake cikin jirgin. Gabanin hakan, yayin wata zantawa da yayi ta wayar tarho da takwaransa na kasar Masar, Mr. Ayrault ya bayyana goyon bayan kasar sa ga mahukuntan Masar, bisa wannin abtila'i da ya faru wanda kuma ya shafi wasu 'yan kasar ta Faransa.

A daya hannun kuma, shugaban kasar Faransa Francois Hollande da takwaransa na Masar Abdel-Fattah al-Sisi, sun alkawarta aiki tare ba kuma tare da wani jinkiri ba, domin tabbatar da halin da jirgin mai lamba MS804 yake ciki.

Jirgin dai na dauke da fasinjoji 56, ciki hadda yaro daya da kuma wasu jarirai biyu, ya kuma bace daga na'urar sadarwa da misalin karfe 2:45 na asubahin Alhamis din nan.

Kamfanin jirgin EgyptAir, ya ce baya ga 'yan kasar Faransa 15, akwai kuma fasinjoji 'yan kasar Masar 30, da 'yan Iran 2. sai kuma 'yan kasashen Birtaniya da Belgian, da Portugal, da Algeriya, da Chadi, da Saudi, da Kuwait, da Sudan da Canada masu fasinjoji daya-daya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v Wani jirgin saman Masar ya bace 2016-05-19 14:22:31
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China