An gano asalin maharin ne ta hanyar tantance hoton zanen yatsunsa, wanda kuma ya dace da takardar shaidar da aka samu cikin motar da ya ke tukawa.
Direban motar dan kasar Faransa ne mai shekaru 31, kuma an haife shi a kasar Tunisiya, amma yana zaune ne a birnin Nice, haka kuma, 'yan sandan kasar Faransa sun taba kama shi bisa laifin mallakar bindigogi da kuma aikata laifin tayar da hankali da kuma sata, amma ba a taba gabatar batun nasa ga hukumar leken asirin kasar ta Faransa ba.
A jiya Alhamis da dare ne, wata motar daukan kaya ta kutsa kai cikin taron jama'a dake kallon wasan wuta albarkacin bikin ranar samun 'yancin kai a birnin Nice dake kudancin Faransa, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 84, yayin da 50 suka jikkata. (Maryam)