Sanarwar ta ce, shugaba Hollande da firaminista Manuel Valls sun gana da wakilan jam'iyyun siyasa dake da kujeru a majalisar dokoki, domin neman ra'ayi kan wani shirin kuduri na gyara tsarin mulki dake da nufin tabbatar da tsaron kasar.
An tayar da jerin ayyukan ta'addanci a ranar 13 ga watan Nuwanban bara a birnin Paris na Faransa, wadanda suka hadddasa rasuwar mutane a kalla 130, yayin da 350 suka jikata, wadanda kuma kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa. A ranar 14 ga watan Nuwanban da ya gabata, fadar shugaban kasar ta sanar da shiga dokar ta baci na kwanaki 12. A ranar 26 ga watan din, ta kara tsawaita wa'adin dokar ta baci zuwa ranar 26 ga watan Faburairu na bana. (Bilkisu)