in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani gungun aiki na MDD yayi allawadai da kisan bakaken fata biyu a Amurka
2016-07-09 12:46:59 cri
Wani gungun aiki na MDD ya fitar a ranar Jumma'a da wata sanarwa game da kisan wasu bakaken fata biyu da 'yan sanda suka yi a kasar Amurka a baya bayan nan, tare da nuna cewa ganin cewa wadanda suka aikata wadannan kisan, duk da shaidun da ake da su, ba a zarge su da laifi ba, wannan shi ne tushen matsala.

Gungun aikin na sanya ido kan matsalar, a ko da yaushe ya bayyana damuwarsa ga gwamnatin Amurka game da kisan bakaken fata da 'yan sanda suke yi tare da yin kiran ganin kotu ta yi aikinta, in ji sanarwar gungun kwararrun MDD kan mutanen dake da asilin Afrika.

A cewar wannan gungun aiki, a kasar Amurka, amfani da karfi kan bakaken fata da 'yan sanda suke yi ya wuce kima, kuma ya zama ruwan dare, domin ya nuna cewa 'yan sanda suna harbi kan bakaken fata fiye da kan fararen fata.

Ana kiran da a gaggauta bincike mai zaman kansa domin tabbatar da ganin an gurfanar da masu hannu cikin wannan matsala gaban kuliya, in ji shugaban gungun aikin na MDD kana kuma akalin musammun kan 'yancin dan adam, Ricardo A. Sunga III.

Sanarwar a fitar da ita a wannan mako, bayan mutuwar Philando Castile a Minnesota, da Alton Sterling a Louisiana, wadanda 'yan sandan Amurka suka harbe, da kuma kisan 'yan sanda biyar a tsakiyar Dallas a ranar Alhamis.

A karshe sanarwar tace "Lokaci yayi, yanzu ga gwamnatin Amurka ta tashe tsaye ta nuna cewa rayuwar bakake tana da muhimmanci da kuma mayar da hakan a matsayin aikin kasa game da wajabcin hana irin wannan kisa a gaba".

Gungun aikin ya kai wata ziyarar aiki a Amurka, a cikin watan Janairun shekarar 2016, kuma zai mika wani rahoton binciken da ya gudanar da kuma shawarwarinsa ga kwamitin hakkin dan adam na MDD a cikin watan Satumban shekarar 2016. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China