in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin waje na kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Faransa
2016-05-16 20:41:42 cri

 

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da takwaransa na kasar Faransa Jean-Marc Ayrault a Litinin din nan a birnin Beijing. Yayin da suke tattaunawa, Wang Yi ya bayyana cewa kasashen Sin da Faransa nada kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, kana dukkansu suna taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya a duniya, suna kuma nacewa ga manufar diplomasiyya ta 'yancin kai, da kokarin inganta yunkurin karfafa dimokuradiyya a huldar kasa da kasa a duniya.

Ya ce huldar dake tsakanin kasashen Sin da Faransa na taka muhimmiyar rawa wajen raya huldar dake tsakanin sauran kasashen duniya.

A nasa bangare Mr. Ayrault cewa ya yi, karfafa hadin gwiwa da daidaitawa da juna tsakanin kasashen Faransa da Sin ya dace da moriyarsu. Ya kuma kara da cewa shugaban kasar Faransa Francois Hollande na fatan halartar taron koli na G20 da za a yi a birnin Hangzhou na kasar Sin. Kaza lika kasar Faransa na da burin ci gaba da kokari tare da kasar Sin, wajen tabbatar da nasarar taron koli yadda ya kamata. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China