in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2016-02-25 10:48:58 cri
A jiya Laraba ne shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a fadar White House dake Washington, babban birnin kasar.

Da farko, Wang Yi ya mika gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Obama, sa'an nan, Wang Yi ya ce, an sami wasu sabbin ci gaba a hadin gwiwar kasashen biyu a karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, kasar Sin tana son ci gaba da yin shawarwari a tsakanin shugabannin kasashen biyu, domin karfafa hadin gwiwar kasashen biyu a game da harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda za a iya magance kalubalen da duniya ke fuskanta cikin hadin gwiwa, haka kuma, kasar Sin tana goyon bayan Amurka kan taron koli game da tsaron nukiliya karo na hudu da za ta yi a karshen watan Maris.

A nasa bangare kuma, shugaba Obama ya nuna fatan alheri ga shugaba Xi Jinping, ya kuma yaba kan hadin gwiwar kasashen biyu ta fuskar harkokin da suka shafi matsalar sauyin yanayi da na shiyya-shiyya. Kaza lika, ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka na da muhimmanci, don haka, ya kamata kasashen biyu su ci gaba da karfafa shawarwarin dake tsakaninsu, yana kuma yi maraba da zuwan shugaba Xi Jiping taron koli na tsaron nukiliya karo na hudu da za a yi a birnin Washington na kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China