in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudaden shigar Afirka sun ragu a shekarar 2015
2016-05-24 13:40:22 cri
Bankin raya Afirka ya fidda wani rahoto game da bunkasuwar tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka na shekarar nan ta 2016, rahoton da ya nuna cewa sakamakon raguwar kudaden da ake shigarwa daga ketare zuwa nahiyar Afirka, adadin wadannan kudade a bara bai wuce dallar Amurka biliyan 208 ba, wanda hakan ya yi kasa da kashi 1.8 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2014.

Haka kuma, rahoton ya nuna cewa, ya zuwa shekarar 2050, kaso biyu bisa uku a al'ummun nahiyar Afirka za su kasance a birane a maimakon yankunan karkara, don haka bunkasuwar birane a nahiyar Afirka na da muhimmancin gaske ga ci gaban Afirka baki daya.

Har wa yau kuma, ko da yake wasu yankuna sun gamu da yanayi na rashin tabbas wajen raya tattalin arziki a mataki na kasa da kasa, da kuma karancin zaman lafiya a wasu yankunan duniya, duk da haka tattalin arzikin nahiyar Afirka ya ci gaba da samun bunkasa cikin yanayi mai kyau a shekarar ta 2015, yayin da nahiyar ta kuma kasance ta biyu da ta fi samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya, baya ga nahiyar gabashin Asiya.

Bugu da kari cikin wannan rahoto, an ce idan aka ci gaba da samun kyautatuwar tattalin arziki a nan gaba, tare da tabbatar karko a fannin cinikayyar farashin manyan hajoji, saurin bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar ta Afirka zai kai kashi 3.7 bisa dari a wannan shekara ta 2016, sa'an nan adadin zai kai kashi 4.5 bisa dari a shekarar 2017.

Bugu da kari, rahoton ya ce, ko da yake kudin shiga a nahiyar Afirka ya ragu da kashi 1.8 bisa dari, duk da haka gwamnatocin kasa da kasa sun samar da karin kudin taimako ga nahiyar har kimanin kashi 4 bisa dari, adadin da ya kai dallar Amurka biliyan 56. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China