Cikin sharhin, Mr. Tian ya bayyana cewa, sabbin matakan da kasar Sin ta dauka domin raya tattalin arzikinta, za su tallafa wa hadin gwiwar Sin da Afirka ta Kudu, haka kuma, bai dace a zargin kasar Sin ba, cewar wasu matakan da ta dauka sun haddasa raguwar farashin hajoji a Afirka, da kuma raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki a nahiyar.
Bugu da kari, ya ce, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana, babban take na manyan shirye-shirye guda goma na hadin gwiwar Sin da Afirka, shi ne karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannonin zuba jari, da habaka masana'antu, a maimakon na fannin musayar ciniki, lamarin da ya sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin su fara zuba jari a Afirka, yanayin da taimaka wa nahiyar wajen gaggauta bunkasuwar harkokin masana'antu, da kuma kyautata kwarewarsu kan ayyukan dake da nasaba da hakan.
Kaza lika, an fidda wadannan manyan shirye-shirye guda goma a lokacin da ya dace a fuskanci kalubaloli da nahiyar Afirka ke fuskanta a sakamakon sauyin yanayin tattalin arzikin duniya. (Maryam)