Babban Sakataren kwamitin tattalin arzikin Afrika na MDD Carlos Lopes, ya bayyana bukatar da ke akwai na 'yan Afrika su duba ainihin dalilan tashin hankali da rashin tsaro a nahiyar domin samun cigaba da kuma inganta ayyukan tattalin arziki.
Carlos Lopes ya bayyana wannan bukatar ce a ranar Larabar nan wajen bikin bude taro na 28 na kwamitin zartarwar kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU. Wanda ake yi karkashin tsarin babban taron kungiyar karo na 26, a cibiyar ta dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Ya ce, rashin daidaito tsakanin kungiyoyi maimakon al'umma watakila shi ne kan gaba na jawo tashin hankali a nahiyar. Yana kuma aiki ne a kan fannoni uku da suka hada da tattalin arziki, walwalar jama'a da siyasa.
Babban Sakataren ya kuma lura da cewa, kin a dama da su shi ne makura a rashin daidaito wanda kuma ya zama babban dalilin dake rura wutar tashin hankali musamman yadda ake kin damawa da matasa.
Mr. Carlos ya bayyana cewar, daga cikin kasashen Afrika guda 54, guda 8 ne kadai har yau ba su taba fuskantar tashin hankali ko rikicin makamai ba tun daga karbar 'yancin kasarsu.
Yanayin tattalin arzikin nahiyar shi ma yana nufin kudin da ake asara a yaki a wani yankin kawai shi ke jawo tsadar tattalin arziki a kasashe makwabta. Wadannan asarori sun hada da damar da ake samu wajen gudun hijira, asarar ciniki, karuwar kudin tsaro, jami'an tsaro da kuma tsadar kula da 'yan gudun hijirar.
Daga nan sai Mr. Carlos Lopez ya jaddada bukatar dake akwai na shawo kan rikici domin samun cigaba da kuma sauyi a nahiyar ta Afrika.(Fatimah Jibril)