Babban masani a fannin tattalin arziki na bankin duniya Francisco yana ganin cewa, ya zuwa yanzu nahiyar Afirka ta kasance daya daga cikin manyan yankuna uku da suka fi samu saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya, kana za ta ci gaba da samun saurin ci gaban tattalin arziki a cikin shekaru 20 masu zuwa. Amma, a waje guda kamata ya yi kasashen Afirka su yi share fage sosai domin tinkarar matsalolin da suka shafi karuwar gibin kudi, tabarbarewar tattalin arziki sakamakon ta'addanci, da kuma yaduwar cutar Ebola, da dai sauransu.
A cikin kasashen Afirka, a matsayinta na kasa ta biyu da ta fi samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a nahiyar, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu ya ragu sosai, wanda ya kai kashi 1 cikin 100 kacal a tsakanin watan Aflilu zuwa Yuni a shekarar 2014. A nata bangaren, kasar Najeriya wadda ta kasance kasa ta farko wajen saurin bunkasuwar tattalin arziki a nahiyar, karuwar tattalin arzikinta ta kai kashi 6.5 cikin 100. Game da sauran kasashe masu karamin karfi, ciki har da Kwadibuwa, Habasha, Mozambique, Tanzaniya da dai sauransu sun tabbatar da saurin ci gaban tattalin arziki a maimakon farfadowar. (Bilkisu)