in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu lissafin kudi sun yi kira wajen yin amfani da nagartattun ma'aunai domin janyo jarin waje a Afrika
2015-08-05 10:56:41 cri

Kwararru a fannin lissafin kudi na duniya baki daya sun yi kira a ranar Talata ga nahiyar Afrika da ta yi amfani da ma'aunai masu nagarta domin samun zarafin janyo karin jarin waje na kai tsaye (IDE).

Darektan kungiyar masu lissafin kudi da aka tabbatar (ACCA) reshen kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, Jamil Ampomah, ya bayyana a birnin Nairobi cewa, ma'aunan lissafin kudi masu karfi na tilasta wa tsare-tsaren da ke kyautata yardar masu zuba jari.

A cikin kasashe da wadannan ma'aunai da ba a aiwatar da su ba da kyau, masu zuba jari na nuna shakku kan bayanan harkokin kudin da aka ba su, hasali ma sai suka rika neman gujewa irin wadannan kasashe, in ji mista Amponah a yayin dandalin koyarwa na ACCA.

Dandalin ya tattara masu samar da bayyana a kai a kai da suke hadin gwiwa tare da kungiyar ACCA domin bunkasa ma'aunan harkokin kudi da lissafi a kasar Kenya.

Mista Amponah ya jaddada cewa ma'aunan lissafi na taka muhimmiyar rawa a wajen cigaban duk wani tattalin arziki.

A cewar darektan ACCA, masu lissafin kudi na iya taka rawa sosai wajen kawar da cin hanci a Afrika.

Cin hanci na daya daga cikin manyan matsalolin da ya kamata nahiyar Afrika ta warware, idan tana bukatar kawar da talauci, in ji shugaban ACCA tare da bayyana cewa, a yanzu haka Afrika na daya daga cikin shiyoyin da ke samun bunkasuwa mafi sauri a duniya. Amma domin gaggauta bunkasuwarta, za ta iya daukar darusa daga kasashe kamar Sin da suka cimma nasarar tattalin arziki tare da yin hadin kai tare da sauran kasashe, in ji Amponah. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China