in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar tattalin arzikin yanki kudu da Sahara za ta kai kashi 3.3 bisa dari a bana
2016-04-13 10:37:42 cri
Kwanan baya, bankin duniya ya fidda wani rahoto kan halin da Afirka ke ciki, inda ya yi hasashe cewa, adadin karuwar tattalin arziki a yankin kudu da hamadar Sahara a shekarar 2016 zai kai kashi 3.3 bisa dari, wanda ya karu idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, wato kashi 3 bisa dari. Kana rahoton ya yi hasashe cewa, za a maido da karuwar tattalin arziki a yankin zuwa kashi 4.5 bisa dari a tsakanin shekarar 2017 da ta 2018.

Haka kuma, bankin duniya ya yi hasashe cewa, karuwar tattalin arziki a yankin Afirka dake kudu da Sahara za ta ci gaba da kasancewa maras karfi. A tsakanin shekarar 2003 da ta 2008, matsakaicin adadin karuwar tattalin arziki a wannan yanki ya kai kashi 6.8 bisa dari, amma a halin yanzu, adadin bai wuce rabin adadin ba.

Bankin duniya ya ce, dalilan da suka haddasa haka a Afirka snna da nasaba da faduwar farashin danyun kayayyaki a kasuwar kasa da kasa, musamman ma man fetur, haka kuma tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba shi ma ya kawo illa kan lamarin.

Bugu da kari, wasu matsaloli kamar su karancin wutar lantarki, tangardar yanayin siyasa, fari da kuma kalubale a fannin tsaro da dai sauransu sun kuma kara janyo illa ga bunkasuwar tattalin arziki a yankin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China