in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shigar karin kamfanonin Sin nahiyar Afirka zai bunkasa tattalin arzikin nahiyar, in ji wasu kwararru
2016-03-04 10:47:52 cri

Shugaban wani kamfanin kasar Sin na kwararru a fannin tattalin arziki Jeremy Stevens, ya ce shigar wasu kamfanonin kasar Sin nahiyar Afirka, zai baiwa kasashen nahiyar damar samun bunkasuwa a fannin kere-kere ko sarrafa kayayyakin masana'antu.

Mr. Stevens wanda ya bayyana hakan jiya a birnin Nairobin kasar Kenya, yayin zantawar sa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya kara da cewa, wasu alkaluman kididdiga sun nuna cewa karuwar saurin bunkasar tattalin arzikin Sin na iya sauka kasa da kashi 6.4 bisa dari da aka yi hasashe a baya, yayin da kuma kamfanonin sarrafa kayayyaki ke kan gaba wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

A irin wannan yanayi a cewar sa, akwai kamfanoni da ka iya juya akalar jarin su zuwa nahiyar Afirka, musamman na bangaren gine-ginen ababen more rayuwa, wanda hakan zai tallafawa nahiyar wajen cimma nasarar bunkasuwa yadda ya kamata.

Mr. Stevens wanda ke cikin mahalarta taron karawa juna sani da aka shirya, game da hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka ta fuskar tattalin arziki, ya ce Afirka na da rawar takawa wajen samar da managarcin yanayin zuba jari, da zai baiwa kamfanonin Sin damar bunkasa bisa sabon yanayin da ake ciki.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China