in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin karuwar tattalin arzikin Afirka dake kudu da Sahara zai ragu, in ji IMF
2016-05-06 11:03:34 cri
Asusun ba da lamuni na IMF ya yi hasashen cewa, a shekarar bana, adadin karuwar tattalin arziki a kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara zai ragu zuwa kashi 3 bisa dari, wanda ya kasance mafi muni cikin shekaru 15 da suka gabata.

Haka kuma, Asusun IMF ya nuna cewa, karuwar bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara a watan Afrilu, ya ragu zuwa kashi 3 bisa dari, amma yanayin karuwar tattalin arziki a ko wace kasa ya bambanta sosai.

Bugu da kari, asusun na IMF ya fidda bayani cewa, duk da kyakkyawan yanayin samun bunkasuwa a wannan fanni, amma adadin karuwar tattalin arziki ba zai kai kashi 6 bisa dari ba, kana saurin karuwar al'ummomi ya fi saurin karuwar tattalin arziki a wannan yanki, lamarin da ya kara matsa lamba ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara.

Dangane da wannan lamarin, shugaban sashen Afirka na asusun ba da lamuni na IMF ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Afirka su kyautata tsarin tattalin arzikinsu, domin samun karin hanyoyin raya tattalin arziki a yankin.

Bugu da kari, asusun na IMF yana ganin cewa, a halin yanzu, akwai kasashe da dama a wannan yanki da ke da karfin raya tattalin arzikinsu, lamarin da ya kawo kyakkyawar makoma ga bunkasuwar tattalin arziki a yankin nan da dan karamin lokaci. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China