in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 3 sun rasu sakamakon fashewar boma-bomai a wata kasuwar Somalia
2016-04-14 10:38:31 cri
Wasu boma-bomai sun fashe a wata kasuwar dabbobi dake kudancin birnin Mogadishu na kasar Somalia a ran 13 ga wata, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla 3, yayin da wasu 6 suka jikkata.

Wadanda lamarin ya faru gaban idonsu sun bayyana cewa, garin da aka kai harin din yana da nisa kimanin kilomita 30 daga babban birnin Mogadishu, kuma dan ta'ddan ya jefa gurnati cikin kasuwar a yayin da mutane suke cikin hada hadar dabbobi, haka kuma, ma'aikatan karbar haraji biyu ne suka rasu a cikin harin.

A yanzu haka jami'an tsaron kasar Somaliya sun dukufa wajen neman maharin da ya gudu bayan tafka wannan danyen aiki.

A halin yanzu, babu wani ko wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin wannan harin ba.

Kwanan baya, sojojin kungiyar AU da rundunar sojojin tsaron kasar Somaliya sun karfafa matakan soja kan kungiyar Al-Shabaab a birnin Mogadishu, lamarin da ya haddasa mai da martanin na kungiyar kansu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China