in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kashe wani madugun kungiyar Al-Shabaab
2014-09-06 16:54:49 cri
Jiya Jumma'a 5 ga wata, gwamnatin Somaliya da ma'aikatar tsaron kasar Amurka sun tabbatar da cewa, madugun kungiyar Al-Shabaab, Ahmed Godane ya mutu a sakamakon harin jirgin saman da sojojin Amurka suka kai a kasar Somaliya.

A wannan rana, fadar shugaban Somaliya ta ba da labari a shafinta na Twitter cewa, madugun kungiyar Al-Shabaab, Ahmed Godane ya mutu a sakamakon harin jirgin saman da sojojin Amurka suka kai a ranar daya ga wata a Somaliya.

Dadin dadawa, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Amurka John Kirby ya tabbatar da wannan batu a cikin wata sanarwar da ya gabatar a ranar Jumma'a, inda ya ce a matsayin muhimmin memba na kungiyar, mutuwarsa za ta kawo babban rauni ga kungiyar sosai.

A ranar daya ga wata ne, sojojin Amurka suka kai harin jirgin sama kan yankin dake kudu da birnin Mogadishu, hedkwatar Somaliya. Rundunar sojan Amurka ta tura jiragen saman yaki da jiragen sama marasa matuki domin kai hari kan wani sansanin Al-Shabaab. Kawo yanzu dai kungiyar Al-Shabbab ba ta tabbatar da kisan shugaban nata ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China