in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mutane da dama a yayin da mayakan Al-shabab suka kama  wani muhimmin gari a Somalia
2014-11-10 16:51:18 cri
An kashe mutane akalla 50, tare da raunata wasu mutane 40 a yayin da mayakan Al-shabab suka kwace iko a garin Kudha, dake kudancin Somalia daga hannun mayakan Raskamboni wadanda ke karkashin gwamnatin Jubba.

Jami'an gwamnatin Jubba sun bada tabbacin garin ya fita daga hannun mayakan Raskamboni. Garin Kudhawanda ke gabar ruwa kusa da kan iyakar Somalia da kasar Kenya yana da mahiummanci ga kungiyar Al-shabab musamman saboda amfanin da take da garin a matsayin tashar ruwa.

Tun farko mayakan Raskamboni, masu biyayya ga gwamnatin Jubba, su ne suka fara kwace garin daga hannnun Al-shabab, makonni biyu da suka wuce.

Kakakin gwamnatin Jubba, Yusuf Mohammed ya bada tabbacin cewar mayakan Al-shabab sun kaddamar da wani gagarumin farmaki a ranar Asabar, inda suka kwace garin na Kudha.

Hussein yace duk da cewa dakarunsa sun janye daga garin saboda dabarun yaki, to amma sojojin zasu koma, kuma za'a ci gaba da aranagama da juna in dai har 'yan kungiyar ta Al-shabab suka ci gaba da kasancewa a yankin.,

A kuma bangare guda kakakin sojoji na kungiyar Al-shabab sheikh Abdulaziz Abu Musa yayi ikirarain cewar, mayakansa sun kashe sojojin gwamnatiun Jubba 63, kamin su kwace iko a garin Kudha.

A kuma daya bangare, jama'ar gari sun bayar da tabbaci cewar dukanin bangarorin biyu, da kuma farar hula, sun yi asarar rayuka a lokacin da akayi bata kashin wanda ya dauki awowi 4 ana fafatawa.(suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China