in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wajen kasar Somalia ya jajantawa kasar Sin bisa rasuwar jami'in tsaron ta
2015-08-05 10:06:55 cri
Ministan harkokin wajen kasar Somalia Abdusalam Omer, ya jajantawa kasar Sin, bisa kisan jami'in tsaron ofishin jakadancin ta dake birnin Mogadishu.

Omer wanda ya bayyana sakon jajen na sa cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, ya ce aukuwar harin da ya sabbaba rasuwar Zhang Nan ya girgiza kasar Somalia. Ministan ya kara da cewa Sin ta dade tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba a Somaliya, tun samun 'yancin kan kasar kawo yanzu.

Daga nan sai ya bayyana kwarin gwiwar sa game da yiwuwar cimma nasarar dakile ayyukan mayakan kungiyar Al-Shabaab, wadda ta dauki alhakin kaddamar da harin na ranar 26 ga watan jiya.

Zhang Nan dake gadi a ofishin jakadancin kasar Sin dake cikin Otel din Al-Jazeera a birnin Magadishu, ya rasa ran sa ne, bayan da aka kai harin kunar bakin wake ga otel din. A ranar Asabar din da ta gabata ne kuma aka maida gawar sa gida Sin domin a binne wa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China