in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan shirin Somalia na sake gina kasa cikin zaman lafiya
2014-06-04 20:47:07 cri
Yau Laraba 4 ga wata ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Somalia Abdirahman Duale Beyle a nan birnin Beijing, domin halartar taron ministocin dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasashen Sin da na Larabawa karo na shida. A yayin ganawarsu, sun amince da muhimmin matsayi na dandalin tattaunawar wajen inganta shawarwari da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da na Larabawa cikin wannan lokaci, kuma sun ce, ya kamata a ci gaba da dukufa wajen ba da babbar gudumawa kan tattaunawar ministoci a taro na wannan karo don samun sakamako mai gamsarwa.

Sa'an nan kuma, Mr. Beyle ya bayyana wa Mr.Wang yanayin da kasar Somalia ke ciki a halin yanzu, inda ya nuna godiya ga taimakon siyasa da tattalin arzikin da kasar Sin ta baiwa kasarsa a lokatan da suka gabata, kuma ya nuna fatan cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Somalia wajen gina hanyoyin zamani da tashoshin jiragen ruwa, da kuma fannin ayyukan noma.

A nasa bangaren kuma, Mr. Wang ya bayyana cewa, kasar Sin na taya gwamantin kasar Somalia murna dangane da manyan sakamakon da ta samu cikin shekaru biyu da suka gabata, kuma kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimako ga kasar yadda ya kamata wajen ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China