in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya nuna juyayi ga masu fama da girgizar kasa a yankin Taiwan
2016-02-08 13:29:33 cri
Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin Xi Jinping yana mai da hankali sosai kan girigizar kasa bisa ma'aunin Richter 6.7 da ta auku a kudancin yankin Taiwan na kasar Sin, ya kuma nuna juyayi ga wadanda suke fama da bala'in.

Xi Jinping ya ce, a safiyar ranar 6 ga wata, girgizar kasa bisa ma'aunin Richter 6.7 ta auku a kudancin yankin Taiwan na kasar Sin, lamarin da ya haddasa babbar asarar dukiyoyi a yankin, har ma wasu mutane sun rasa rayukansu sakamakon bala'in, shi ya sa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali matuka kan yanayin da yankin yake ciki, tare da kuma nuna juyayi ga wadanda suke fama da wannan bala'in da ya auku, kaza lika, tana nuna ta'aziya ga wadanda suka rasu cikin bala'in, tare da nuna samar da taimako ga 'yan uwanmu na yankin ta fannoni daban daban.

Bugu da kari, bisa kididdigar da hukumar kwana-kwana ta birnin Tainan dake kudancin Taiwan ta yi, an ce, ya zuwa karfe 9 na yau ranar 8 ga wata, girgizar kasa din da ta auku ta riga ta haddasa rasuwar mutane guda 37. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China