Mr. Hong ya fadi haka ne yayin da yake ba da amsa game da zaben da aka yi jiya a yankin Taiwan, inda madam Tsai Ing-wen ta lashe zaben ta zama sabuwar jagorar yankin Taiwan.
Mr. Hong Lei ya kara da cewa, batun Taiwan harkar cikin gida ce ta kasar Sin. Ya kasance Sin daya tak a duniya, babban yanki da yankin Taiwan dukkansu wani bangare ne na kasar Sin. Kasar Sin ba za ta yarda da a taka ikon mulkinta da cikkaken yankinta ba. Sakamakon zaben da aka samu a yankin Taiwan ba zai canja wannan hakikanin abu da ra'ayi daya da kasashen duniya suka samu gaba daya ba. Ko da yake an samu sauye-sauyen halin da ake ciki a tsibirin Taiwan, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan matsayin kasancewar Sin daya tak a duniya, kuma ba ta amince da matakin neman ballewar yankin Taiwan ko kasancewar Sin biyu a duniya ba. A kan wannan batu mafi muhimmanci dake shafar ikon mulkin kasa, da cikakken yankin kasar, niyyar gwamnatin Sin tana da kauri kamar babban dutse. Ba za ta yarda da a dauki kowane irin matakin neman ballewar Taiwan daga kasar Sin ba. (Sanusi Chen)