Ma'aikatar harkokin harkokin cikin gida ta kasar da hukumar rage aukuwar bala'u ta kasar sun aika da jami'ai domin aikin ceto a wannan yankin, tare da yin kira da a samar da kayayyakin jin kai. Ya zuwa yanzu an riga an aika da tantuna 1,000 a wajen.
Fiye da sojoji da masu kayan sarki 500 daga sansanin Soji na Lanzhou sun riga sun isa wajen domin taimakawa wajen neman wadanda bala'in ya rutsa da su. Har ila yau jami'an kiwon lafiya 22 su ma an aika da su wannan yankin na Pishan.